Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gizgizar Kasa Ta Hallaka Mutane 300 Da Jikkata 2,500


Wata girgizar kasa da ta afkawa sassa dake kan iyakar Iraq da Iran a jiya Lahadi ta kashe fiye da mutane 300 tare da raunata mutane 2,500.

A yau Litinin kafar yada labarai ta Iran ta bada rahoton cewa mutane 328 ne suka mutu, kuma yawancin waddanda bala'in ya rutasa da su mazauna garin da ake kira Sarpol-e-Zahab a lardin Kermanshah.

Masu aikin ceto da agaji sun yi ta aiki a cikin daren har zuwa yau Litinin domin taimakwa waddanda girgizan kasar ta afkawa.

Hukumar kula da yanayin karkashin kasa ta Amurka ta ce karfin girigizar ya kai maki 7.3, kuma ta samo asali ne a kusa da garin Halabja a yankin Kurdawan Iraqi.

Frime Minista kasar Haidar al-Abadi, ya ce ya umarci hukumomin kiwon lafiya da na agaji, su dauki dukkan mataki na taimakawa wadanda bala'in ya shafa

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG