Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Mutum 26 Da Suka Mutu A Hatsarin Kwale-kwale A Neja


Kaburburan wasu daga cikin mutanen da aka yi jana'izarsu (Facebook/Haruna Saidu Kinbokun)
Kaburburan wasu daga cikin mutanen da aka yi jana'izarsu (Facebook/Haruna Saidu Kinbokun)

Hatsarin ya faru ne da misalin karfe takwas na safiyar ranar Lahadi yayin da mutanen ke kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu, a cewar hukumomi.

Rahotanni daga jihar Nejan Najeriya na nuni da cewa an yi jana’izar mutum 26 da suka rasa rayukansu a wani hatsarin kwale-kwale da ya auku.

Hatsarin ya faru ne yayin da wasu manona ke kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu a karamar hukumar Mokwa.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe takwas na safiyar ranar Lahadi a cewar hukumomi.

Bayanai sun yi nuni da cewa mutanen da suka mutu galibinsu mata ne da kananan yara.

Sun kuma taso ne daga yankunan Gbajibo, Ekwa da Yankyade daga karamar hukumar ta Mokwa.

“Adadin mutanen da suka mutu ya tsaya a 26, mafi akasarinsu mata da kananan yara ne yayin da an ceto akalla mutum 30.” Wata sanarwa da Sakataren yada labaran karamar hukumar ta Mokwa Abdullahi Alh. Abubakar Dakani ya fitar a ranar Lahadi ta ce.

Sanarwar ta kara da cewa, aikin ceton na hadin gwiwa ne da ya hada da gwanayen ninkaya daga yankin tare da ma’aikatan hukumar kai daukin gaggawa na jihar ta Neja.

A tsakiyar watan Yuni mutum 108 sun rasa rayukansu a hatsarin kwale-kwale a yankin jihar ta Neja.

Hukumomi sun ce galibin abin da ke haddasa hatsarin na da alaka da diban mutanen da suka wuce kima da rashin saka rigar hana nutsewa a ruwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG