Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana’izar Jakadan Najeriya a Qatar


Dr. Abdullahi Bawa Wase

Gabanin nada shi a matsayin jakadan Najeriya a kasar ta Qatar, Dr. Wase wanda masani ne kan harkar tsaro, ya sha ba da gudunmuwa a shirye-shiryen Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) kan batutuwan da suka shafi tsaro.

Rahotanni daga Najeriya na cewa an yi jana'izar Jakadan Najeriya, Dr. Abdullahi Bawa Wase a Doha, babban birnin Qatar.

A jiya Juma'a Dr. Wase ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar ta nuna yadda shugaba Muhammadu Buhari ya jinjinawa Dr. Wase wanda kafin rasuwarsa shi ne jadakan Najeriyar a kasar ta Qatar.

Wase dan asalin jihar Filato ne, kuma tuni gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya bayyana mutuwar ta sa a matsayin babban rashi ga kasar baki daya.

Da safiyar ranar Asabar, wata sanarwa daga ma'aikatar harkokin wajen Najeriya dauke da sa hannun mai magana da yawun ma'aikatar, Tope -Elias Fatile, ta bayyana cewa a birnin na Doha za a yi jana'izar mamacin kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Gabanin nada shi a matsayin jakadan Najeriya a kasar ta Qatar, Dr. Wase wanda masani ne kan harkar tsaro, ya sha ba da gudunmuwa a shirye-shiryen Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) kan batutuwan da suka shafi tsaro.

A watan Yulin 2016, shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin jakadan Najeriya a kasar ta Qatar.

Ku saurari dan takaitaccen tsokacin da Dr. Wase ya yi a watan Yunin 2016 a rahoton da wakilinmu Ibrahim Abdulaziz ya hada kan matsalar satar mutane a jihar Taraba a wancan lokacin:

please wait

No media source currently available

0:00 0:00:41 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG