Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yi kira ga kasashen duniya su maida hankali kan yakar talauci tsakanin matan karkara


Mata a kasashen duniya

Kasashe a duk fadin duniya suna bukin tunawa da ranar mata ta duniya, inda ake yaba ci gaban da mata suka samu a fannin kasuwanci, da siyasa, da kuma ilimi

Kasashe a duk fadin duniya suna bukin tunawa da ranar mata ta duniya, inda ake yaba ci gaban da mata suka samu a fannin kasuwanci, da siyasa, da kuma ilimi. Sai dai babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yace ci gaban da aka samu bai isa ba.

A cikin sanarwar da ya bayar yau Alhamis, babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniyan ya yi gargadi da cewa, har yanzu akwai aiki tukuru a gaba, kafin mata da ‘yan mata su iya more damar da maza suke da ita. Mr. Ban Ki-moon yace banbancin da ake nunawa mata da kananan ‘yan mata yafi tada hankali a yankunan karkara, wadanda sune kimanin kashi daya bisa hudu na adadin al’umma a duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, kimanin mata miliyan dubu dari biyar da suke aiki a kananan gonaki ko kuma masu aikin kwadago suna baya a fannin tattalin arziki, da rayuwar yau da kullum da kuma harkokin siyasa. Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce za a sami inganci a abincin da ake nomawa a duniya baki daya idan mata suka sami dama da jari kamar maza.

Sun kuma ce tabbatar da ganin mata a yankunan karkara suna samun tallafin zai taimaka waken yakar yunwa.

Shugabar hukumar kare hakkokin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay ita ma tayi kira ga gwamnatoci su kara himmatuwa a wannan yunkurin. Bisa ga cewarta, gaza cin moriyar baiwar da mata suke da ita, ba alheri bane ga kasashen duniya.

A Amurka, sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen kasar, Hillary Clinton da kuma uwargidan shugaban kasa Michelle Obama zasu mika lambobin yabon karfin hali ga mata daga kasashe goma na duniya da suka hada da Afghanistan, da Pakistan, da Burma da Sudan da kuma Columbia. Sauran kuma sune, Libya da Saudiya da Maldives da Turkiya da kuma Brazil.

Wani jami’in ma’akatar harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa, za a bada lambobin yabon ne domin nuna irin gagarumar rawar da mata ke takawa ga habakar tattalin arzikin kasashen dake tasowa da kuma zaman lafiya da ci gaban kasa.

XS
SM
MD
LG