Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Korafi Akan Halayyar Alhazan Najeriya


Alhazai sun taru kusa da birnin Makka mai tsari a Saudiya.

Yayin da sarkin Muri Alhaji Abbas Isa Tafida mataimakin amirul Hajjin bana ya yaba da aikin Hajin da amincewa da kurakurai wasu kuma korafi suka yi akan alhazan.

Yayin da yake jawabi Alhaji Abbas Isa Tafida ya godewa duk alhazan da suka yi aikin hajjin bana.

Yace su wakilan gwamnatin tarayya sun yi aikinsu tsakaninsu da Allah haka ma na jihohi. Amma ya amince akwai kurakurai da aka yi. Duk da kurakuran yace an samu cigaba.

To saidai shugabar kamfanin jirgin yawo na Dije Travels wadda kamfaninta yayi jigilar alhazai Hajiya Amina Ibrahim tana ganin wasu alhazan basu fahimci mahimmancin aikin hajji ba. Tace halayar alhazan a Saudiya babu dadi. Ta kira jama'a su dubi halinsu su canza domin aikin hajji ba aikin wasa ba ne. Aiki ne kamar aikin yaki. Komi mutum zai bari ya fuskanci aikin.

Tace mutane sun zo aikin hajji ba hakuri ba kimantawa babu tausayi kuma basu san yakamata ba. Duk da fadakarwa da ake yi kullum bata canza zani ba.

Saidai su jami'an Saudiya sun inganta aikin hajjin bana. Sun kawo wasu sauye-sauye lamarin da ya rage cunkoson jama'a a wasu wurare.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG