Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Nasarar Kulla Yarjejeniyar Tsagaita Wuta a Libya


MDD tayi nasarar shiga Tsakani da ya kai ga cimma yarjejeniyar kawo karshen arangama da aka yi na tsawon mako guda a Tripoli babban birnin kasar Libya.

An sanar da haka ne bayan da hukumomin kasar Libya suka bayyana cewa adadin wadanda suka rasu a rikicin ya karu zuwa sittin da daya, yayin da da dama kuma suka ji raunuka.

Gwamnatin Amurka da kasashen Birtaniya, da Faransa da kuma Italiya sun fitar da sanarwar hadin guiwa inda suka yi na’am da tsagaita wutar

Fada ya barke a Tripoli ne ranar ishirin da bakwai ga watan Agusta bayan da wata kungiya dauke da makamai dake Tarhouna mai tazarar kilomita sittin da biyar kudu maso gabashin babban birnin kasar, ta kaddar da harin ba zata kan wata kungiyar mayaka da suke gaba da juna.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG