Accessibility links

An yi taron Fulani Makiyaya na shekara a Birnin Kebbi cikin jihar Kebbin Najeriya inda suka bayyani irin matsalolin da suke fuskanta a kasar.

An yi taron Kungiyar Fulani na kasa da aka fi sani da Miyetti Allah a Birnin Kebbi babban birnin Jihar Kebbin Najeriya inda Fulani suka bayyana irin matsalolin da suke fuskanta a duk fadin kasar.

Shugaban kungiyar Alhaji Bello Abdullahi Bodejo ya ce kungiyar ta kusa gama gagarumin tantance duk matsalolin dake addabarsu a kasar Najeriya da kuma yadda za'a warwaresu. Yayin da yake jawabi shugaban kungiyar ya ce rashin shugabanci ne shi ya tura Fulani cikin rudani. Ya ce shugabanni cutarsu suke shi ya sa Fulani suka pansama cikin daji a duk fadin Najeriya. Wannana shi ne sanadiyar samun rigingimu ko ina domin basu da shugabanni masu adalci. Yanzu ne kungiyar ke neman adalan shugabanni da zasu iya tafiyar da al'amuran abubuwan da suka shafi Fulani. Ya ce amma akungiyance suna samun shugabannin a jihohi kafin su zo kan na kasa gaba daya.

Shugaban kungiyar ya ce akwai rubuce-rubuce da suka yi wa gwamnonin jihohin da abun ya shafa da ma gwamnatin tarayya amma wasu gwamnonin basu da karfin gwiwar yin abun da yakamata domin wata manufa ta siyasa.Ya ce ba batun shugabancin Fulani ba ne kawai. Wanda zai yi hakan ya sansu? Ya san matsalolinsu? Ya ce dole sai shugaba ya san wadannan abubuwa kafin ya iya magancesu. Ya ce an jahilci Fulani domin ba'a san menene matsalarsu ba.

Da yake bada bayani game da matsalolin sai ya ce daya daga cikinsu itace batun zama 'yan kasa. Ya ce a wasu wuraren korarsu ake yi ana cewa su ba 'yan kasa ba ne. Shugaban ya ce ka dubi Fulani ka ce shi ba dan kasa ba ne tamkar renin wayo ne. Ya yi misali da gwamnatin Pilato inda aka kori Fulani kuma har yau ana faman yin fada da su. Ya ce har yanzu ana kan korar Fulani daga jihar Pilato. Amma ya ce babu wani dalili da za'a ce su Fulani ba 'yan kasa ba ne. Ya ce duk inda Fulani suka zauna to ya zama nasu. Idan suna da dabbobi su yi kokari su sayi wurin. Wannan shi ne fadakarwar da suke yi wa Fulani. Ya tabo batun kokarin da majilisar tarayya take yi ta cire batun bako da dan kasa a kundin tsarin kasar Najeriya.

An kammala taron da rantsar da sabbin shugabannin kungiyar na kasa.

Murtala Faruk Sanyinna na da rahoto.

XS
SM
MD
LG