Accessibility links

An Yi Taron Share Fagen Taron Kolin Tattalin Arzikin Arewa Maso Gabas


Kwararru a fannoni dabam-dabam na raya tattalin arziki daga arewa maso gabas sun gana a Abuja domin tsara taron kolin da zasu yi wata mai zuwa a Gombe

Kwararru daga fannoni dabam-dabam na raya tattalin arziki a jihohi 6 na yankin arewa maso gabashin Najeriya, sun gana a Abuja domin tsara taron kolin bunkasa tattalin arzikin yankin da ake shirin gudanarwa a farkon wata mai zuwa a garin Gombe.

Uku daga cikin wadannan jihohi, watau Borno da Yobe da Adamawa, su na karkashin dokar-ta-baci, wadda ta nakkasa ayyukan tattalin arziki. Rashin tsaron da ya janyo kafa dokar-ta-bacin, yana barazanar haddasa yunwa a saboda manoma da dama sun kasa shuka kayan abincin da suka saba.

Wannan yanki na arewa maso gabas, shi ne cibiyar ayyukan kungiyar nan ta Boko Haram mai yakar hukumomin Najeriya.

Jihohin na yankin arewa maso gabas, zasu gudanar da taron kolin bunkasa tattalin arzikinsu, daga ranar 3 ga watan Disamba a Gombe.

Wanda ya shugabanci taron share fagen na abuja, Dahiru Buba Beri, yace yana da muhimmanci a janyo hankalin shugabannin yankin game da bukatar bunkasa noma a zaman wata hanya sadidan ta yakar talauci da rashin ayyukan yi da kuma magance rashin tsaro a wannan yanki.

Jami'ai da dama sun halarci wannan taro sun kuma yi bayani a kan yadda zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin arewa maso gabas da kawo karshen fitina, kamar yadda za a iya ji cikin wannan rahoto na Nasiru Adamu Elhikaya.

XS
SM
MD
LG