Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Sun Gwabza Da 'Yan Bindiga A Jihar Bauchi


Dakarun na gwamnati sun tare 'yan bindigar a garin Gadar Maiwa, bayan da suka samu labarin cewa sun doshi garin Azare domin kai hari a can.

Jami'an tsaro a Jihar Bauchi sun ce sun kashe dan bindiga guda daya, sun kuma kama hudu a wata arangamar da aka yi ta tsawon lokaci a dab da garin Gadar Maiwa dake yankin karamar hukumar Ningi, a kan hanyar Bauchi zuwa zuwa Kano.

Haka kuma, rundunar 'yan sandan jihar ta ce sun samu bindigogin kai farmaki samfurin AK-47 guda 11, da bindigar harba roka ko gurneti, da rokoki 3 da kuma harsasai fiye da dubu daya.

Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Bauchi, DSP Haruna Mohammed, yace jami'an tsaro sun samu bayanin cewa akwai wasu 'yan bindiga da makamai cikin motoci da suka doshi garin Azare domin kai farmaki. A dalilin haka ne sai jami'an tsaro suka yi musu kwanton-bauna dab da garin Gadar Maiwa

An ce akwai wasu daga cikin 'yan bindigar da suka tsere, kuma jami'an tsaro su na binciken yankin ko zasu iya kamo su.

Babu tabbas a kan ko su wanene 'yan bindigar, koda yake wasu kafofin dabam su na bayyana su a zaman 'yan kungiyar nan ta Boko Haram.
XS
SM
MD
LG