Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Taron Shekara-shekara Na Harkokin Shari'a Na Jihar Borno


Taron Shekara-shekara na harkokin shari'a
Taron Shekara-shekara na harkokin shari'a

Wannan taron shi ne irinsa na farko cikin shekaru biyar saboda rikicin Boko Haram da ya addabi jihar, yayi kaca-kaca da ita, tsaro ya tabarbare kana rayuka da dama suka salwanta banda wadanda suka rasa muhallansu.

Yayinda yake jawabi alkalin alkalan jihar Borno Justice Kashim Zanna yace batun rikicin Boko Haram a jihar bai kawo karshe ba sai lokacin da matan da suka rasa mazajensu sun koma cikin hayacinsu.

Justice Zannan yace tabbatar da cewa matan da aka kashe mazajensu sun koma cikin hankalinsu a cikin muhallansu a garuruwansu aiki ne da ya ratawa akan kowa a jihar kuma ya zama wajibi. Yace rikicin ba zai kawo karshe ga kowa ba sai dubban marayun da aka bari sun dawo cikin jama'a ba tare da wata rayuwar kunci ba. Saboda haka hakkin kowa ne a tabbatar cewa marayun sun dawo cikin jama'a cikin natsuwa da samun cigaba.

Justice Zanna ya kira jama'ar jihar da su san irin taimakon da gwamnatin tarayya da na jihar su keyi wurin sake gina garuruwan da 'yan Boko Haram suka rugurguza da kokarin tallafawa al'umma, lamarin da yace ba karamin aiki ba ne.

Kwamishanan Shari'ar jihar Barrister Kaka Shehu Lawal ya bayyana mahimmancin taron. Yace na daya suna son su shaidawa duniya sun fara samun zaman lafiya dalilin farfado da taron ke nan.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG