Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Taron Tantance Kamfanonin da Zasu Yi Jigilar Alhazan Bana


Musulman Najeriya
Musulman Najeriya
An yi taron tantance kamfanonin jiragen saman da zasu yi aikin jijgilar alhazan Najeriya na bana zuwa Saudiya.

Barrister Abdulahi Mukhtar kwamishanan zirga-zirgan jirage na hukumar alhazan Najeriya yace duk wanda ya bayyana gaban hukumar ba tare da shiri ba to ko kamfanisa ya fadi ke nan ba zai samu jigilar alhyazan ba. Barrister Mukhtar ya yi furucin ne a taron tantance kamfanonin da suka cancanta su yi jigilar alhazai su dubu 76,000 bana.

Barrister Mukhtar yace za'a bincika bayanan kwarewar kamfanin jirgi kafin a bashi aikin. Tambaya nan ita ce gazawar kamfanonin cikin gida ya sa hukumar alhazan ta gayyato kamfanonin kasashen waje? Muhammed Musa Bello shugaban hukumar yace da kamfanonin waje suna gudun su zo su yi jigilar alhazan Najeriya amma kila sun zo ne yanzu domin sun lura cewa Alhajin Najeriya ya canza.

Yanzau Alhajin Najeriya ya san ya kamata. Ya san ciwon kansa kuma yana da ladabi da bin dolokin Najeriya da na Saudiya. Saboda haka kamfanonin kasashen waje suna sha'awar a yi jigilar da su. Kwamitin zai binciki kamfanonin da suka rubuta takardar neman aikin ko suna da jirage ko babu. Za'a tambayi hukumar Najeriya ko ta tabbatar jiragen kamfanonin suna da izinin yin shawagi a sararin samaniya na Najeriya da kuma na Saudiya. Duk sai an tabbatar suna da jirage kuma zasu iya yin jigilar cikin tsanaki, lafiya da lumana. Bayan haka ne za'a zauna dasu a tattauna kan nawa zasu yi jigilar.

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG