Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

JNI Tace An Mayarda Musulmai 'Ya'yan Bora a Zaben Wakilan Taron Kasa


Alhaji Muhammed Sa'ad Abubakar Mai Martaba Sarkin Musulmi
Alhaji Muhammed Sa'ad Abubakar Mai Martaba Sarkin Musulmi
Kungiyar Jama'atul Nasril Islam ta yi watsi da yadda aka mayarda Musulmai baya wurin zabar wakilan taron kasa duk da cewa su ne suka fi yawa a kasar.

Kungiyar Jama'atul Nasril Islam tace ita ba zata amince da banbancin da aka nunawa al'ummar Musulmai wajen zabo mahalarta taron kasa ba. Dr Khalil Aliyu Abubakar sakataren kungiyar na kasa yace suna cikin bakin ciki da yadda aka mayarda al'ummar Musulmi 'ya'yan bora.

Inji Dr Abubakar Musulmai su ne kashi hamsin cikin dari na duk al'ummar Najeriya yayin da Kirista ke da kashi arba'in. Amma abun mamaki sai gashi an baiwa Musulmai kashi 35 na wakilan Kirista kuma nada kashi 60.

Shi kuma Barrister Dalong yana ganin wadanda suka shirya taron basu damu da matasan kasar ba. Yace inda taron na kasa ne yakamata matasa su kasance suke da wakilai kashi 60 cikin 100. Bayan matasan dattawa su kasance kashi 20 mata kuma kashi 20. Da an yi hakan to da sai a ce an hada al'umma. Yace amma wadanda aka zabo zuwa taron kashi 80 cikinsu mutane ne da shekarunsu suka kama daga 60 zuwa sama. Yace wannan kamar an yiwa matasa fashi ne. Yace wadanda aka zabo mutane ne da ake zarginsu da gazawa a zamanin jiya. Wato yanzu an kawosu ne su karasa barnar da basu gama yi ba ko kuma an kawo su ne a biyasu domin su shirya taimakawa a zaben 2015? Rashin ba matasa zarafi a taron babban illa ne. Idan kuma ba'a maida hankali ba yana iya sa kasar cikin hatsari

Barrister Dalong ya cigaba da cewa matasa ne basu da aikin yi idan sun je neman aiki kuma su mutu. Su ne basu da abinci mai kyau. Za'a kuma yi taro dominsu amma ba'a sasu cikin taron ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG