Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Taron 'Yansanda da Amintattu Domin Inganta Tsaro A Adamawa


Taron 'yansanda da amintattu domin inganta tsaro a jihar Adamawa

Kwamishinan yan sanda na jihar Adamawa Musa Kimo ya kaddamar da taron amintattu don zana jaddawalin kyautata hulda tsakanin jami'an 'yan sanda da farar hula don yaki da aikata miyagun ayuka, fashi, satar mutane da keta dokokin kasa a Yola fadar jihar Adamawa.

Taron da ya wakana sanadiyar yunkurin babban sifeto janar na yan sandan Najeriya Ibrahim Idris na shawo kan matsalolin tsaro da kasar ke fama dashi, musamman a jihohin arewa maso gabashi.

Yankin yana fuskantar barazanar ayukan ta'addanci daga kungiyar Boko Haram kungiyar da ta kara kaimi wajen kai hare-hare a jihar.

Muryar Amurka tayi fira da wasu cikin mahalarta taron kuma ta fara taunawa da

shugaban 'yan banga na jihar Adamawa Dr, Murtala Aliyu wanda ya ba da

shawarwari ta yadda wannan sabon shirin zai dore ya kuma inganta tsaro a yankin arewa maso gabas musamman jihar Adamawa.

Shi kuwa Alhaji Sabo Magaji gani yake akwai bukatar

a kyautata aikin kananan 'yansanda masu hulda da jama'a yau da kullum ta hanyar da zasu himmatu su kuma dauki ayyukansu da mahimmanci ta kiyaye

tsaron lafiya da dukiyoyin jama'a.

Da yake mayarda martani wamishinan yan sanda na

jihar Adamawa yace hukumomi na daukan matakan da suka wajaba da zummar kawar da duk wani aika-aika.

Ga rahoton Sanusi Adamu da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

XS
SM
MD
LG