Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yi Wani Taro Tsakanin Shugaba Buhari da Shugabanin Majalisar Kasa


Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari da Shugaban Majilisar Dattawa Sanata Bukola Saraki.

Taron abunda aka saba yi tsakanin bangarorin Gwamnatin biyu ne.

An yi wani taro na sulhu tsakanin shugaba Muhammadu Buhari, da shugabanin majalisar kasa domin warware duk wata takaddama ko rashin fahimtan dake tsakanin bangarorin biyu.

Bisa ga kiran da majalisar wakilan ta Najeriya tayi a kwananan cewa ya kamata a shiga tsakani domin a sulhunta bagarorin biyu domin kada alamuran demokradiya su ci gaba da durkushewa a kasar.

Koda yake ba’a bada wata sanarwa takamammiya dangane da wannan taron ba shugaban Majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki, ya bayanawa manema labaru cewa taron da aka saba yi tsakanin bangarorin Gwamnatin biyu.

Ba’a kira wannan taron domin tattauna wani abunda aka fara harsashe ba ko maganar Ministoci ko kuma wata takaddama da akayi hasashe ba.

Wani kwararre aka sha’anin majalisa Farfesa al-Mustapha Osuji, ya ce wannan ganawa da bangarorin biyu suka yi yana da mahimmaci domin zai taimaka wajen habaka demokradiya a Najeriya, da kuma baiwa kowane bangare yancin sa ,domin shi shugaban majalisar dattawa shine shugaban majalisa baki dayan ta a tsarin zaman majalisa kuma idan aka ce basu ganawa da shugaban kasa abun na iya kawo cikas.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG