Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korafe Korafe Akan Ahmed Musa Ibeto


Ginin majalisun tarayyar Najeriya

A jahar Neja ra’ayin ‘yan siyasa ya sha banban akan bayana sunan Ahmed Musa Ibeto a jerin sunsyen da aka turawa majalisa

Bayan da majalisar dattawan Najeriya, ta bayana sunayen mutane 21, da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya tura mata domin tantance su a matsayin ministoci, a yanzu haka ‘yan Najeriya, na ci gaba da yin tsokaci akan wadannan mutane.

A jahar Neja, ra’ayin ‘yan siyasa ya sha banban akan bayana sunan tsohon mataimakin Gwamnan jahar Ahmed Musa Ibeto, a cikin jerin sunayen da shugaba Buhari ya turawa majalisar.

A halin yanzu dai yayin da ake jiran kashi na biyu na sunayen sabbin ministocin da shugaba Buhari, ya ce zai turawa majalisar nan gaba.

Amma masu nazari harkokin siyasa na ganin akwai bukatar Karin akalla mata guda uku da kuma matasa ‘yan kasa da shekaru 40, akalla suma guda uku bisa la’akari da gaggarumi gudumawar da suka barai wajen kafa sabuwar Gwamnatin Muhammadu Buharin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

XS
SM
MD
LG