Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Watsi Da Mahaifar Sardauna


Ahmadu Bello
Ahmadu Bello

Duk da habbaka arewacin Najeriya da Sardaunan Sakkwato ya yi, hukumomin yankin da sauran daidaikun mutane masu sukuni sun yi watsi da mahaifarsa, sabanin yadda ake ta habbaka mahaifar wasu da ba su ma yi ko kusan abin da ya yi ba a cewar masu korafi.

Wannan Jumu'a ce cikar shekaru hamsin da biyar bayan kisan Firimiyan lardin Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello Sardauna da wasu shugabanni na wannan lokacin a juyin mulki na farko da soji suka yi a shekarar 1966.

Ana ci gaba da tunawa da Sardauna amma dai mutanen mahaifarsa da ke Sakkwato sun ce ba su gamsu da yadda aka sakawa masa ba akan hidimar da yayi wa al'umma.

Sardauna of Sokoto
Sardauna of Sokoto

Abubakar Yusuf, Dan Masanin Rabah, wanda ya yi magana da yawun Masarautar Rabah, mahaifar Sir Ahmadu Bello Sardauna, ya nuna yadda aka fita batun gidan na Firimiya, a maimakon a yi wani abu a mahaifarsa don nuna cewa da gaske ake.

Su ma dangin Sardauna dake zaune a garin har yanzu sun tofa albarkacin bakinsu kan sadaukarwar da yayi wa Najeriya. Sun nuna bukatar a nuna kaunar Sardauna ta wajen raya mahaifarsa.

Abubakar Bala Rabah, Yariman Rabah, shi ma Jigo ne kuma mazaunin garin na Rabah. A Rana irin wannan kungiyoyi sukan shirya taruka domin tunawa da sadaukarwa da Firimiya yayi wa yankin Arewa da Najeriya baki daya.

Zaidu Bala Kofa Sabuwa shi ne shugaban kungiyar muryar Talaka ta kasa wadda takan shirya irin wadannan tarukka a kowace shekara.

Yanzu dai shekaru 55 Sir Ahmadu Bello Sardauna baya duniya amma yanzu ana tuna shi, abinda wasu ke ganin bai rasa nasaba da gaskiya da adalci da yayi a lokacin shugabancinsa Wanda kuma abin koyi ne ga shugabannin wannan lokaci.

Ga Muhammad Nasir da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00


Karin bayani akan: Ahmadu Bello​, Sardaunan Sakkwato, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG