Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Yankar Rago Ma Mutane 4 ‘Yan Gida Guda


Wasu 'yansandan Najeriya
Wasu 'yansandan Najeriya

A cigaba da aukuwar abubuwan ban takaici na kashe-kashen mutane a arewacin Najeriya, wasu masu ragaggen imini sun bi dare su ka hallaka mutane 4 'yan gida guda a wani kauye.

Wasu ‘yan bindiga, wadanda ba a san ko su waye ba, sun bi dare su ka yi yankar rago ma mata da miji da biyu daga cikin ‘ya’yansu. A wani al’amari mai nuna kamar su na da dan ragowar Imani, ‘yanbindigar sun bar yaro dan watanni 9 da haihuwa da ransa.

‘Yanbindigar dai sun abka ma gidan ne bayan da su ka fantsama cikin kauyen wajen karfe 2 :00 na asuba, yayin da wannan iyali ke barci kamar akasarin mutanen kauyen, mai suna Mbayi da ke cikin karmar Hukumar Takum ta jahar Taraban Najeriya.

Mai magana da yawun Rundunar ‘Yansandan jahar Taraba, ASP David Misal ya tabbatar ma wakilinmu Ibarhim Abdul’aziz faruwar wannan abin takaicin. Ya ce kafin Rundunar ‘yansanda ta sami labari daga jama’a miyagun sun gama aika-aikar har sun gudu. Ya ce amma Kwamishinan ‘yansandan jahar Taraba ya umurci DPO da AC na yankin da su tattara bayanai game da al’amarin.

Ga dai Ibrahim Abdul’aziz da cikakken labarin:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG