Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Yankar Rago Ga Wasu Miyagu 11 A Kurfi


Barayi Da Masu Sace Mutane Da Aka Kama Kawanan Baya a Najeriya.

Rana ta baci ma wasu miyagu su wajen 11, a daidai lokacin da su ke kan tsara wata ta'asa a karamar Hukumar Kurfi ta jihar Katsina a Najeriya.

Dubun wasu miyagun da ke daji a jihar Katsina ta cika, bayan da aka rada ma 'yan sintirin yankin wurin da su ke wani taro da zummar kai wani hari. Bayan arangamar da aka yi dai, Allah ya dora 'yan sintiri kan miyagun, wadanda aka masu yadda su kan yi ma bayin Allah.

Dama 'yan sa Kai da suka harzuka da hare-haren 'yan bindiga a yankinsu, suna sa ido tare da lura da abubuwan dake gudana, wanda hakan ya kai su ga far ma wadan da suke zargin mahara ne, a inda suke tattauna a tsakaninu.

Saboda harzukar da su ka yi da danyen halin miyagun, sun kashe su ta hanyar yankasu, baya ga sauran matakan da akan dauka kan irin wadannan miyagun.

Majiyar Muryara Amurka, wadda ta bukaci sakayawa, ta bayyana cewa saboda tsabar sa ido da kuma lura da kai komon jama'a, gami da hadin kai da jama'a ke bayarwa, ta kai ga samun bayanan sirri cewa wasu da ake zargin mahara 'yan bibdiga ne, suna taro a bayan gari, shi ne 'yan sa kai suka shirya su ka kai masu farmaki tare da aikawa da su lahira.

Ga Sani Shu'aibu Malumfashi da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00


Facebook Forum

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG