Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Zanga-Zanga a Australia Duk Da Gargadi kan Yaduwar Corona


Zanga-zanga a kasar Australia

Dubban mutane a kasar Australia sun yi watsi da gargadin yiwuwar zanga-zangar mutane da dama ta janyo barkewar cutar COVID-19, inda su ka bazu kan tituna a fadin kasar jiya Asabar don nuna goyon baya ga kungiyar fafatukar ‘yanto 'yancin bakake ta “Black Lives Matter” biyo bayan mutuwar wani ba-Amurke bakar fata wanda wani dan sanda farar fata ya danne masa wuya.

Masu zanga-zanga sun yi gangami a manyan birane irinsu Sydney da Melbourne da kuma kananan garuruwa a fadin kasar bayan da, shekaran jiya Jumma’a, wata kotu ta yi watsi da wani hukuncin da aka yanke tun farko mai cewa yin zanga-zanga a kasar ya saba ma doka saboda barazana ga lafiya.

Australian Prime Minister Scott Morrison gestures during a press conference at Australia's Parliament House in Canberra on March 22, 2020. - Morrison told citizens to cancel any domestic travel plans to slow the spread of coronavirus, warning stronger mea
Australian Prime Minister Scott Morrison gestures during a press conference at Australia's Parliament House in Canberra on March 22, 2020. - Morrison told citizens to cancel any domestic travel plans to slow the spread of coronavirus, warning stronger mea

(Firaministan Australia Scott Morrison)

Masu macin na rike da kwalayen da ke dauke da sakonni masu cewa, “Ba na iya numfashi,” wanda daya ne daga cikin kalamai na karshe da ba-Amurke bakar fatar nan George Floyd ya yi amfani da su ranar 25 ga watan Maris yayin da wani dan sanda ke ta danne masa wuya da gwiwa bayan da aka kayar da shi a kasa da ankwa a hannunsa.

Wani sakon kuma na cewa, “Labari iri daya, kasa daban daban,” wanda ke nuni da irin banbancin launin fata da ke kasar ta Australia, al’amarin da ya kai ga mutuwar jinsin ‘yan asalin kasar da ake kira Aborigine, wadanda aka kuma fai jefawa kurkuku.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG