Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Zanga Zanga a Wajen Gangamin Trump


Wasu Masu adawa da Donlad Trump a gaban 'yan sanda

Kusan masu zanga zanga dubu ne suka yi dandazo tare da raira waka a wajen wani babban dakin taro da ke San Diego, yayin da Donald Trump da ake tunanin zai yiwa jam’iyar Republican takarar shugabancin Amurka, ya ke jawabi ga magoya bayansa.

Masu zanga zangar, wadanda ke dauke da totocin Amurka da na kasar Mexico, sun yi fito-na-fito da ‘yan sanda a birnin na San Diego da ke kudancin California.

Akalla nisan kilomita 24 daga kan iyakar Mexico zuwa Amurka, inda kaso mafi tsoka na mazauna yankin al’umar Latino ne.

‘Yan sanda sun ce sun cafke mutane da dama, ciki har da wani mutum da ya tsallake wani shinge daga aka gindaya tsakanin masu zanga zangar da ‘yan sanda.

A baya Trump ya yi ikrarin cewa zai duba yiwuwar gina wata katafariyar Katanga tsakanin Amurka da Mexcio saboda dakile kwararar da bakin haure ke yi zuwa cikin Amurkan.

XS
SM
MD
LG