Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Talata Shugaban Amurka Zai Yi Jawabi Akan Danganta Tsakanin Kasarsa da Vietnam


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Ziyarar shugaban Amurka Barack Obama a kasar Vietnam ta shiga tarihi domin ita ce ta farko cikin shekari arba'in da daya da kasashen biyu suka daina yaki da juna

A yau Talata ne ake sa ran shugaban kasar Amurka Barack Obama, zai yi jawabi a birnin Hanoi, wanda ake tsammanin zai mayar da hankali kan batutuwan da zasu inganta dangantakar Amurka da kasar Vietnam da bukatar tattaunawa mai ma’ana tsakanin kasashen biyu.

Jami’an fadar White House sunce, shugaban zai bayyana muhimmancin tattaunawa tsakanin kasashen biyu a lokacin da suka sami sabani, ciki harda maganar ‘yancin dan Adam. Haka kuma a yau Talatar ne Obama zai gana da wasu masu gwagwarmayar rajin kare hakkin bil Adama, har ma da wasu kananan yan kasuwa.

Sai dai kuma kungiyoyin kare hakkin bil Adama na cewa Obama yayi azarbabi wajen take lamarin cin zarafin dan Adam da akayi, a kokarinsa na maido da dangantakar Amurka da Vietnam.

Jiya Litinin ne Obama ya sanar da cewa Amurka ta ‘dagewa Vietnam dadadden takunkumin nan na hana sayarwa Vietnam makamai.

Shugaban kasar Vietnam Tran Dai Quan, yayi maraba da wannan shiri na kawo karshen rashin jituwar.

Shugaban Amurka a Vietnam
Shugaban Amurka a Vietnam

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG