Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Zanga-Zanga Yau A Fadin Kasar Sham


Wani dan zanga-zanga yana kokarin kwanto kusa da gawar wani da aka harbe, domin kaucewa harsasai na dakarun tsaron kasar Sham a birnin hama

Shaidu da ‘yan gwagwarmaya sun ce an kashe akalla mutane 10 yau jumma’a bayanda dakaru suka bude wuta kan masu zanga zanga.

Dubun dubatan 'yan kasar Sham, ko Syria, sun gudanar da zanga zangar kin jinin gwamnati yayinda dakarun tsaro suka fadada murkushe ‘yan hamayya.

Shaidu da ‘yan gwagwarmaya sun ce an kashe akalla mutane 10 yau jumma’a bayanda dakaru suka bude wuta kan masu zanga zanga. Bisa ga cewarsu an kashe galibin mutanen ne a kusa da Damascus, babban birnin kasar.

Masu zanga zangar kin jinin gwamnati sun kuma yi gangami a wadansu birane da suka hada da Homs, Dara’a, Deir, El-Zour da kuma Qamishi. An gudanar da zanga zangar ce a wannan jumma’ar farko da fara azumin watan Ramadan.

XS
SM
MD
LG