Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yiwa Sama Da Mutane Miliyan 3 Rigakafin Cutar Sankarau a Jihar Naija


Ana bada rigakafin cutar sankarau
Ana bada rigakafin cutar sankarau

An yi ma mutane sama da miliyan 3 alurar rigakafin cutar sankarau a jihar Naija.

An yi ma mutane sama da miliyan 3 alurar rigakafin cutar sankarau a jihar Naija. Ma'aikatan kiwon lafiya sun dauki kwanaki goma suna gudanar da rigakafin a kananan hukumomi guda ashirin da biyar da ke jihar.

Kafin daukar wanan matakin bada rigakafin cutar sankarau da gwamnatin Najeriya ta bada umurni ayi, an samu wadanda suka fara kamuwa da cutar a jihar Naija kuma mutum guda ya rasa ranshi.

Wani direktan ma’aikatar lafiya a jihar Naija, Dr. Iya Bage Aliyu, ya yi bayani cewa mutum daya ne kawai ya rasa rai daga cikin mutane shida da suka kamu da cutar sankarau a jihar. Ya kuma ce gwamnatin tarraya ce ta dauki matakin gudanar da allurar rigakafin, ba jihar Naija ba ce. Ya kuma ce, “Ana yin gangamin ne a wuraren da ake kira meningitis belt, inda ake yawan samun sankarau.”

Dr. Aliyu ya ce, babu fargabam sake barkewar sankarau a jihar. Ya fadi cewa alurar da suka bayar zata kiyaye jama’an da suka karbi rigakafin har zuwa shekara goma.

Wakilin Sashen Hausa Mustafa Nasiru Batsari ya aiko da rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG