Accessibility links

Yau ce ranar tunawa da mahimmancin masai ga kowane gida a fadin duniya.

Ranar goma sha tara ta watan Nuwamban kowace shekara Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin jawo hankalin jama'a dangane da mahimmancin masai ga kowane gida a fadin duniya.

Hukumomin kiwon lafiya a duniya sun tabbatar da cewa ana samun bullar cututtuka irin su ciwon amai da gudawa ko kolera a sakamakon yin bahaya barkatai a filin Allah.

Wata mai magana Malama Saratu ta ce wasu basu san mahimmancin tanadar da masai ba ga kowane gida. Don haka kebe rana irin ta yau zai taimaki irin wadanna mutanen su sani. Ta ce idan ba makewayi a gida to gidan ya zama wuri mai kazanta koina kuma a cikin gidan zai ta yin wari kana kuma a damu makwafta. Rashin wurin kewayawa ko masai a gida yakan haddasa zawo da amai har ma cutar ta yadu cikin jama'a.

A nasa jawabin Abdul Jibril Kakaki mazaunin birnin Minna jihar Neja ya ce yana da makewayi a gidansa. Ya ce ko a addinance yakamata mutum nada wurin kewayawa inda zai tube cikin siri ya yi tsarki kana ya fito ba tare da nuna tsiraici a waje ba.

Sai dai har yanzu hukumomi a jihar Neja na wayar da kawunan mutane kan mahimmancin gina masai a gida tare da hukunta duk wadanda aka samu sun bujirewa fadakarwar. Kawo yanzu kusan mutane talatin ake gurfanar dasu gaban kotu a kowane wata domin laifin rashin gina masai a gidajensu in ji Zubairu Abubakar Maguma mataimakin shugaban tsaftace muhalli ta jihar Neja.

Binciken da masu kiwon lafiya a duniya suka gudanar ya nuna cewa a cikn yara biyar dake mutuwa daya na mutuwa ne sanadiyar rashin bahaya.

Mustapha Nasiru Batsari nada rahoto.

XS
SM
MD
LG