Accessibility links

An yiwa wadansu mata 18 masu yoyon futsari tiyata a Cross River


Wadansu mata masu jinya

Asusun bunkasa kasa da kasa Amurka USAID ya kaddamar da cibiyar jinyar masu yoyon futsari a babban asibitin Ogoja a jihar

Asusun bunkasa kasa da kasa Amurka USAID, tare da hadin guiwar gwamnatin jihar Cross Rivers ya kaddamar da cibiyar jinyar masu yoyon futsari a babban asibitin Ogoja a jihar.

Da yake jawabi yayin kaddamar da cibiyar jinyar masu yoyon fitsarin, manajan ayyukan jinyar yoyon futsari na USAID a Najeriya cif Iyeme Efem ya bayyana cewa, wannan cibiyar ita ce ta tara da aka kafa tare da tallafin kasa da kasa. Bisa ga cewarshi, wannan cibiyar zata kula da mata masu yoyon futsari a jihar Cross Rivers da kuma kewaye.

Cif Efem ya bayyana cewa, kimanin mata 150, 000 ne suke fama da cutar yoyon futsari a Najeriya, yayinda ake samun kimanin mata 12, 000 dake kamuwa da cutar kowacce shekara. Ya kuma bayyana takaicin ganin cewa, daga cikin wannan adadin kimanin 4, 000 kadai ake yiwa tiyata a shekara.

Matan da aka yiwa tiyata a sabon asibitin da aka bude sun bayyana irin wahalhalun da suka sha sakamakon kamuwa da wannan ciwo inda wadansu aurensu ya mutu yayinda da dama suka zama tamkar marayu sakamakon kyama da wariya da ake nuna masu sabili da halin da suka shiga.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG