Accessibility links

Masu dauke da kwayar cutar HIV sun nemi a daina nuna masu wariya


Ana gwada jini a cibiyar binciken kanjamau

Masu fama da cutar kanjamau sun yi kira da a daina nuna masu wariya a wajen daukarsu aiki a kasashe dabam dabam na duniya

Masu fama da cutar kanjamau sun yi kira da a daina nuna masu wariya a wajen daukarsu aiki a kasashe dabam dabam na duniya. Masu fama da wannan cutar da suka gudanar da jerin gwano a manyan tituna birane dabam dabam na jihar Nija dake tarayya Najeriya albarkacin ranar kanjamau ta duniya, bayan sun bayyana farin cikinsu domin kebe rana musamma da nufin maida hankali kan wannan cuta da masu fama da ita, sun kuma bayyana korafe -korafensu.

Shugaban kungiyar masu dauke da cutar kanjamau na jihar Naija, mallam Sama’ila Garba ya bayyana cewa, da dama daga cikinsu suna da karfin yin kowanne irin aiki, amma da zarar an san suna dauke da cutar, sai a kyamace su a ki daukarsu aiki.

A nashi korafin wani mai dauke da cutar ya bayyana cewa, tallafin da ake bayarwa da sunansu, baya kaiwa garesu. Bisa ga cewarshi, wadansu mutane dabam suke karba su ci. Yayinda kuma bisa ga cewarshin ake watsi da su idan kuma ana wani taro ko wani shiri da ya shafe su. Ya bayyana cewa, masu fama da cutar basu halartar tarukan gangamin ranar kanjamau sabili rashin damawa da su, yayinda wadansu da dama kuma suke da sha’awar zuwa sai dai basu da hali.

Dr. John Chama likitan dake kula da masu fama da cutar sida a jihar Naija, ya bayyana cewa, babu shakka akwai butakar ganin tallafin da ake samu daga kasashe kamar Amurka yana kaiwa ga masu fama da cutar. Bisa ga cewarshi, kamata ya yi a bi masu fama da cutar har gida domin a tallafa masu.

Gwamnatin jihar Naija, ta bakin alhaji Baba Umaru babban sakataren hukumar yaki da yaduwar cutar a jiha, ya bayyana cewa, akwai masu fama da cutar a gwamnati da basu fita su bayyana kansu, yayinda kuma wadansu da dama suka hada kansu da kungiyoyin da aka kafa domin tallafawa masu fama da cutar. Bisa ga cewarshi, duk wadanda suka fita fili suka nemi taimako ana taimaka masu iyaka iyawa.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG