Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yiwa Wani Dan Gudun Hijira Yankan Rago A Barno.


Wasu 'yan gudun hijira a jihar Barno

Wannan al'amari dai ya auku ne a daya daga cikin sansanonin 'Yan gudun hijira dake Maiduguri babban birnin jihar Barno. Akwai jami'an tsaro da aka girke a wanan sansanin, baya ga jami'an tsaro an kewaye sansanin da katanga.

Wani dan uwan wanda aka kashen ya gayawa manema labarai cewa sun rabu da dan'uwan nasa a daren Laraba, amma da aka wayi gari basu ganshi ba.

Rahotanni suka nuna cewa a dai dai lokacinda suka gano gawarsa ne kuma, jami'an tsaro suka kama wani mutum da ake zargin yana da hanu ko kuma shine ya kashe matashin.

Wannan sansanin yana dauke da mutane sama da dubu 10.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG