Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yiwa wasu 'yansandan jihar Rivers kwantan bauna an kashe biyar cikinsu


Solomon Arase, babban sifeton 'yansandan Najeriya
Solomon Arase, babban sifeton 'yansandan Najeriya

Wasu 'yan bindiga daga jihar Bayelsa sun yiwa 'yansandan jihar Rivers kwantan bauna yayinda suke dawowa daga jihar Yobe kan hanyarsu ta komawa jihar Rivers din inda suke aiki

A wata sanarwa dake da sa hannun kakakin rundunar 'yansandan jihar Rivers DSP Ahmed Muhammed, tace lamarin ya faru ne a garin Okobe dake cikin jihar Bayelsa.

Jami'an 'yansandan da aka kashe suna komawa jihar Rivers ne yayinda suke dawowa daga jihar Yobe inda aka turasu zuwa yin wani aiki na musamman.

Sanarwar tace lamarin ya kara bayyana a fili irin wahalu da barazanar da jami'an 'yansanda ke fuskanta wajen aiwatar da ayyukansu na yau da kullum.

Rundunar ta jihar Rivers tace ba zata bata lokaci ba wajen farauta da kamo wadanda suka aikata wannan danyen aikin.

A makon jiya ne dai wasu masu tada kayar baya suka kai wani mummunan hari akan kamfanin mai na kasar Amurka, wato, Chevron.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG