Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar 'yansandan jihar Jigawa ta kama wani da makamai


Solomon Arase babban sifeton 'yansandan Najeriya

Rundunar 'yansandan jihar Jigawa ta sanar da kame wani Emma Gwadal da bindigogi da albarusai a cikin motarsa da yace zai kaiwa wani mai suna Sylvesta Gofwel dake zama a Kafin Hausa

Emma Gwadal ya shaidawa 'yansanda cewa wani Dembo Akpa ne daga jihar Filato ke kera musu bindigogin.

DSP Abu Jinjiri kakakin 'yansandan jihar Jigawa yace sun kama shi Sylvesta din wanda ya yadda shi ne za'a kaiwa bindigogin amma basu samu nasarar kama mai kerawa ba.

Bayan sun kammala bincike sun gurfanar da mutanen biyu gaban kotu. Yanzu suna fuskantar shari'a.

Sakamakon binciken da 'yansanda suka yi bai nuna mutanen nada alaka da 'yan Boko Haram ba ko kuma wata kungiya ta 'yan fashi da makami.

'Yansanda na tuhumar mutanen biyu da laifin mallakar makamai ba kan ka'ida ba. Mallakar irin wadannan makaman ba tare da lasisi ba laifi ne.

To cajin da ake yiwa mutanen biyu ka iya canzawa saboda har yanzu basu cafke mai kera makaman ba. Tana yiwuwa idan an kamashi wasu bayanai su canza da ka iya kaiga canza cajin da ake yi masu yanzu.

Tun farko babban sifeton 'yansanda Najeriya Solomon Aease ya bada umurnin kara wa'adin sabunta lasisin mallakar bindigogi zuwa watan gobe.Bayan wa'adin duk wanda bai sabunta nashi ba 'yansanda zasu soma kamasu

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG