Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zabi "Farmajo" a Matsayin Sabon Shugaban Somali


Farmaajo

'Yan majalisar kasar Somali sun zabi sabon shugaban kasa a yau Laraba, inda suka zabi tsohon firaminista mai shaidar dan kasashe biyu, wato Amurka da Somali.

An bayyana Mohammed Abdullahi Mohammed, wanda aka fi sani da “Farmajo” a matsayin wanda yayi nasara bayan kada kuri da yan majalisu suka yi a zagaye na biyu a Mogadishu.

Farmajo ya lashe mafi yawan kuri’un da aka kada a karo na biyu, wanda ya baiwa Shugaban dake kan karaga a yanzu Hassan Sheik Mohamud da kuma tsohon shugaban kasa Sheikh Sharif Ahmed tazara mai yawa.

Mohamud ya amince da shan kaye bayan da aka kammala kidaya kuri’un, lamarin da ya sa taron mutane dake wurin suka barke da sowa a cikin babban filin jirgin saman Mogadishu.
Wadanda suka shaida lamarin sun fadawa Sashen Somaliya na Muryar Amurka cewa sowa da murna da aka yi har da harba bindigogi ya barke akan tituna a cikin babban birnin Somalin.

Nan take dai aka rantsar da sabon shugaban kasar wanda ya sha alwashin samar da cikakken tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da kuma taimakawa talakawa.

XS
SM
MD
LG