Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi China Da Hannu a Bacewar Wasu 'Yan Jarida


Wani dan majalisar dokokin Amurka na kira ga Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar da ta bukaci China ta gudanar da bincike kan bacewar wasu ‘yan jaridar kasar uku, wadanda suka fara kwarmata illar cutar coronavirus a birnin Wuhan.

A wata wasika da ya rubuta, dan majalisar wakilai na jam’iyyar Republican Jim Banks, ya yi kira ga gwamnatin Amurka da ta nemi a yi bincike kan makomar Fang Bin da Chen Qiushi da kuma Li Zehua.

Bisa ga rahotannin kafafen yada labarai, sun bace ne bayan da suka dauki hotunan bidiyo suka kuma kafe su a yanar gizo, ciki har da hotunan cunkoso a asibitoci da kuma wasu tarin gawarwaki a wata karamar motar bas.

Banks ya rubuta cewa “baki daya mutanen uku sun fahimci irin hatsarin da suka saka kansu, wajen fitar da rahotanni kan coronavirus a China, amma suka yi duk da haka.”

Banks dai na zargin gwamnatin China da daure su a gidan yari, ko kuma wani abin da ya fi hakan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG