Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana amfani da kaciya wajen wayar da kan jama’a dangane da illar cutar kanjamau a kasar Zimbabwe


Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe

Wadansu ‘yan majalisar dokokin kasar Zimbabwe guda hudu sun yi kaciya a yunkurin wayar da kan al’umma dangane da illar cutar kanjamau

Wadansu ‘yan majalisar dokokin kasar Zimbabwe guda hudu sun yi kaciya a yunkurin wayar da kan al’umma dangane da illar cutar kanjamau.

‘Yan majalisar wadanda suka fito daga manyan jam’iyun siyasar kasar dake adawa da juna, Jam’iyar shugaba Robert Mugabe, ZANU-PF da kuma ta Firai Minista Morgan Tsvangirai, MDC, sun dauki matakin hadin guiwar a yunkurin shawo kan cutar.

Binciken Hukumar lafiya ta duniya na nuni da cewa, yiwa maza kaciya yana rage hadarin kamuwa da kwayar cutar HIV da kasshi 60%.

Kasar Zimbabwe tana amfani da wannan hanyar wajen yaki da cutar kanjamau da tayi kamari a kasar.

A shekarar alib da dari tara da casa’in kasar Zimbabwe ce tafi kowacce kasa a duniya yawan masu fama da cutar kanjamau, yayinda aka sami kimanin kashi 13.7% na mutanen da suka balaga a kasar dauke da kwayar cutar a 2009.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG