Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Barin Wuta a Gabas Ta Tsakiya


Fafatawar da ake yi tsakanin Isira'ila da Falasdinawa

Yayin da duniya ke kiran bani-Yahadu da 'yan kawunnensu, Falasdinawa, su kai zuciya nesa, abin sai dada faskara ya ke yi. Luguden wuta kan juna sai abin da ya karu, yayin da rayuka ke kara salwanta baya ga asarar dukiyoyi daga bangarorin biyu.

Firaministan Isira’ila Benjamin Netanyahu, ya ce ya bai wa rundunar sojin kasar umurnin cigaba da kai hare-haren jiragen sama kan ‘yan gwagwarmaya da makami da ke Gaza, da kuma umurnin tura tankokin yaki da atilare da sojoji zuwa kan iyakar Gaza din.

‘Yan gwagwarmaya da makamin sun yi ta harba rokoki jiya Asabar daga Zirin Gaza wanda je karkashin ikon Hamas zuwa kudancin Isira’Ia.

Isira’ila kuma ta mai da martani da hare-haren jiragen sama da tankokin yaki. Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ce Falasdinawa hudu sun mutu, ciki har da wata mata mai ciki da wani jinjiri. Isira’ila ta ce ta hallaka ‘yan gwagwarmaya da makami guda 8.

Rokokin Hamas din sun hallaka wani dan Isira’la sannan akalla wasu mutane hudu sun ji raunuka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG