Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Binciken Israila Akan Mutuwar Falasdinawa 29


Gangamin Falasdinawa akan iyaka da Israila
Gangamin Falasdinawa akan iyaka da Israila

Kotun kasa da kasa ta kira a kawo karshen tashin hankali tsakanin Israila da Falasdinawa bayan da Falasdinawa 29 suka rasa rayukansu lamarin da kotun ta ce tana bincike akai amma kuma Israila ta ce babu ruwanta da kotun domin ita ba mamba ba ce

Biyo bayan mutuwar Falasdinawa 29 a wata zangar zangar da suka yi arangama da yan sandan Isra’ila a kwanan nan, kotun kasa da kasa mai binciken manyan laifuka ta ICC tayi kira ga kawo karshen zubda jinin a zirin Gaza.
Fatou Bensouda tace dama ofishinta yana gudanar da wasu bincike da farko a yankin Falasdinawar, don haka tana sa ido sosai a kan yankin.
Tace duk wani laifi da ake zargin aikatawa a yanayin da ake ciki a Falasdinu, akwai yiwuwar gabatar da kara ga ofishinta ya tantance.
Rahotannin sun nuna ana binciken Isra’ila a kan mutuwar Falasdinawa 29 yayin wata zanga zangar kwanaki 10 da kuma arangamar da aka samu a kan iyakar zirin Gaza.
Isra’ila ba mamban kotun ba ce kuma ta musunta cewa Falasdinu ba kasa ba ce, don haka bata da hurumin shiga wannan kotun.


Kotun ICC itace kotun duniya guda daya mai cin gashin kanta dake binciken manyan laifukan yaki. An kafata ne a shekarar 2002domin tayi binciken kisar kare dangi,da laifukan yaki da kuma laifukan da aka yiwa bil adama.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG