Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Bukatar Hadin Kai Domin Kawo Karshen Zubda Jini a Najeriya


Sansanin 'Yan Gudun Hijira Na Gaggawa a Zamfara
Sansanin 'Yan Gudun Hijira Na Gaggawa a Zamfara

Masana sun bukaci hadin kan al'umma da gwamnatoci don kawo karshen zubda jini da aka kwashe fiye da shekaru 20 ana yi a jihar Filato da wasu sassan Najeriya.

A taron manema labarai da suka yi da sunan kungiyar masana da manazarta daga cibiyoyin ilimi dabam-dabam a jihar Filato, kungiyar ta ce ta lura cewa sau da dama wasu na fakewa da sunan fadan makiyaya da manoma suna satar dabbobi, da fashi da makami, da yakin kwatar kasa, da yin sojin gona da sauransu wajen kawo rarrabuwar kawuna da kisan wadanda basu ji basu gani ba.

Shugaban kungiyar, Farfesa Danladi Atu daga Jami'ar Abuja, ya ce sun kira taron manema labarai ne domin su taimaka wajen jawo hankalin duniya cewa, ya kamata a duba inda matsalar ta ke a kuma yi gyara.

"Damuwar shine kashe-kashen da ake yi. Mun ga yadda abubuwa suke tafiya sai tada tabarbarewa take yi," inji Farfesan.

Ya ce asalin wannan rikici ya taso ne tsakanin makiyaya da manoma saboda yadda Najeriya ta kasance babu tsari, dole ne a samu damuwa.

"Inda suke bi a da, wuraren yanzu babu su. Idan aka duba tafkin Chadi, shi ma ya fara bushewa." Ya ce kamata yayi gwamnatin tarayya ta duba wannan matsalar.

Ya ci gaba da cewa, a cikin wannan yanayi ne wasu suka samu damar fakewa da wannan rikicin makiyaya da manoma domin cimma burinsu.

Haka ma Malama a cibiyar fasaha ta jihar Filato, Madam Magdalene Agwom ta ce a yanzu haka mata da yara da dama suna fama a sansonin 'yan gudun hijira.

"A yi hakuri, abin da hakuri bai bayar ba, fada ba zai bayar ba!" inji Madam Agwom

Ta ci gaba da cewa, kamata yayi a hada hannu,

"A lokacin da muke yara, Fulani idan suka zo gonakinmu sai su yi mana taki don mu samu a yi noma kuma yayi kyau," ta ce amma yanzu babu irin wannan zaman.

Sakataren hadin kan dukkan kabilun Jihar Filato, Peden Lugujar ya ce sun lura cewa siyasa ya shiga rikicin jihar Filato.

Ya ce da gani za a gane cewa siyasa ta fara shiga ciki kuma su na da niyyar kiran 'yan siyasa domin jan kunnensu.

"Zamu kira 'yan siyasan kuma in baka zo ba, zamu nuna maka cewa muke da mutanen don haka zamu hadu da kai a rumfar zabe," inji sakataren.

Saurari rohoton

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG