Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cece-Kuce Kan Auren Wani Dattijo Da Karamar Yarinya A Jihar Naija


 Alhaji Yakubu Umar Mainasara da Amaryarsa Adama Amad
Alhaji Yakubu Umar Mainasara da Amaryarsa Adama Amad

Hukumar Kula da kare Hakkin Mata da yara kanana a jihar Nejan Nigeria tace ta fara gudanar da bincike akan auren wani Dattijo Dan Kimanin Shekaru 61 Mai suna Alhaji Yakubu Umar Mainasara dake Zaune a garin Lapai da kuma wata yarinya da aka ce tana da karancin Shekaru.

Kafofin Sadarwa na zamani ne dai suka fara yayata labarin wannan aure da suka ce yarinyar yar shekaru 15 ce. Sai dai iyayen yarinyar sunce shekarunta 20 da watanni 11.

A cikin hirarta da Sashen Hausa,Barista Maryam Kolo, shugabar hukumar kare hakkin Mata da yara kanana a jihar Neja, tace sun samu labarin auren kuma suna gudanar da bincike akan lamarin. Ta kuma yi alkawari cewa zasu dauki Matakin da ya kamata da zarar sun gano akwai Matsala a auren.

A nashi bayanin, dattijon ya bayyana cewa, abinda yafi damunshi shine, yadda ake yayata auren nashi a kafofin sadarwa da kuma bata mashi suna. Ya bayyana cewa, bai ga wani laifi ba a auren yarinyar kasancewa ba shi bane mijinta na farko, saboda haka baya ganinta a matsayin karamar yarinya duk da karancin shekarunta.

Babban wan yarinyar wanda ya bada aurenta bayan an biya sadakin Naira dubu dari uku ya tabbatar da cewa yarinyar ta haura shekaru 20 kuma kasancewa aurenta na uku kenan ba za a yi batun shekarunta ba, kuma ba a tirsasa mata ta auri dattijon ba.

Da yake tsokaci kan batun, babban daraktan ma’aikatar kula da harkokin addinai ta jihar Neja Dr. Umar Faruk Abdullahi yace auren bai sabawa shari’ar Musulunci ba.

Saurari cikakken rahoton:

Auren wani dattijo da karamar yarinya0#;30"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG