Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cecekuce Akan Dokar Hana Kulle 'Yan Jarida A Nijar


Majalisar Dokokin Nijar
Majalisar Dokokin Nijar

Dokar hana kulle dan jarida saboda bada labarin da bai yiwa wani dadi ba a Nijar ta samo asali daga ayar dokar da shugaban gwamnatin rikon kwarya Janar Salun Jibo ya sakawa hannu a shekarar 2010 a matsayin gudummawar karfafa diflomasiya a kasar Nijar

To saidai shekaru shida bayan kafa dokar 'yan jarida na cewa kwalliya bata biya kudin sabulu ba.

Bubakar Jallo mai fafutikar kare hakkin 'yan jarida yace ko a wannan shekarar akwai wasu 'yan jarida har gidan kurkuku aka kaisu. Yace su su ce an taka hakkin 'yan jarida alkalan kasar kuma su ce ba'a taka hakkinsu ba. Yace yawancin lokaci idan 'yan jarida suka tona asirin wani mai iko sai ya nuna shi yana da ikon hukumtasu ko musguna masu. Yace wannan ba komi ba ne son rai ne kuma an sha yinshi a kasar Nijar.

Amma shugaban hukumar tace labaru Abdulrahaman Usman na cewa idan an bi ta barawo a bi ta mai bin sawu. A cewarsa akwai 'yan jaridan dake bata rawarsu da tsalle. An samu 'yan jarida dake hada kai da 'yan ta'ada domin a samu tashin hankali saboda akwai dokar da ta hana a kulleshsu.

Kafa kwamitin hadin gwuiwa tsakanin gwamnati da kungiyar 'yan jarida ita ce hanya daya tilo da ka iya warware jainja da cecekucen da ake yi kamar yadda hukumomi da 'yan jarida suka yi amanna da hakan. Yin hakan zai sa su 'yan jarida da hukumomin shari'a zasu gane abu guda.

Ga rahoton Souly Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG