Wani tsohon babban kwamandan kungiyar al-Shabab, yayi Allah wadarai da mummunan harin bam da ya kashe mutane akalla 276 ranar asabar a Mogadishu, babban birnin kasar.
Mukhtar Robow, tsohon mukaddashin Amir na al-Shabab, yayi wannan tur a yau litinin lokacin da ya ziyarci asibitin Medina dake Mogadishu domin bayar da gudumawar jinni. Yace wannan harin na rashin Imani ne, kuma mummunan bala’i.
Ya shaidawa ‘yan jarida cewa mutanen dake da hannu a wannan ba zasu taba shiga Aljanna ba a saboda suna zub da jinin mutanen da bas u jib a, bas u gani ba.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin bam din, wanda shine guda daya mafi muni da aka taba kaiwa a tarihin Somaliya. Amma gwamnatinS omaliya da kwararru kan ta’addanci sun yi imanin cewa kungiyar al Shabab ce ta kai.
Facebook Forum