Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Zanga-zanga a Amurka


Wasu masu zanga-zanga kenan a Amurka
Wasu masu zanga-zanga kenan a Amurka

An shirya ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin cin zarafi da ‘yan sanda su ke yi da kuma nuna wariya launin fata, makwanni uku kenan bayan mutuwar George Floyd a jihar Minnesota, kuma ‘yan kwanaki bayan da dan sanda ya harbe Rayshard Brooks a Atlanta.

Zanga-zangar ta yau Litinin ta hada da yin gangami a Majalisar Dokokin jihar Georgia, da kuma haduwa a wajen fadar White House inda makonni biyu da suka gabata jami’an tsaro suka tarwatsa masu zanga-zangar lumana, kafin shugaban kasa Donald Trump da mukarrabansa suka taka zuwa wata majami’a domin daukar hoto.

Haka kuma yau Litinin, hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD ta amince da gudanar da muhawara ranar Laraba akan ko nuna banbancin launin fata ya taka rawa wajen cin zarafin bil Adama da cin zarafin ‘yan sanda da kuma yin amfani da karfi kan masu zanga-zangar lumana.

Jiya Lahadi an gudanar da zanga-zanga a birane masu yawa, ciki har da birnin Washington da New York da Los Angeles da Atlanta da kuma birnin Miami

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG