Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Kai Samame Kan Kusoshin Kungiyar IS


Ana ci gaba da kai samame akan manyan shugabannin kungiyar IS a Siriya, wani abu da ke nuna gaggawar da ake yi na ganin an kawar da kusoshin kungiyar ta ‘yan ta’adda.

Dakarun gamayyar mayakan SDF da ke kawance da Amurka, wadanda suka taka rawa wajen kawar da shugaban kungiyar ta IS, Abu Bakr al-Baghdadi, da kuma kakakin kungiyar, Abu Hassan al-Muhajir, sun ce an kai wasu jerin hare-hare a ranar Larabar da ta gabata da nufin kawar da manyan shugabannin kungiyar ‘yan ta'addan, inda aka neme su da rai ko a mace.

Kakakin mayakan na SDF, Mustapha Bali ya wallafa a shafin Twitter a jiya Litinin cewa, "an yi nasarar kai wani samame tare da kama wasu manyan shugabannin kungiyar ta ISIS.”

Sannan ya ce wadanda ba a kashe su ba za a kama su, yana mai cewa laifukan da kungiyar ta Daesh ko kuma IS ta aikata ba za su tafi a banza ba.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG