Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci gaba Da Kokarin kashe Gobara A Wani Bene A London


Gobara A Birtaniya
Gobara A Birtaniya

Babban kwamandan 'yan sanda na London ya tabbatar da cewa ya zuwa yanzu an samu gawarwaki 6, amma adadin zai karu da zarar an fara duba cikin ginin

‘Yan kwana-kwana a London sun ci gaba da yakar daya daga cikin gobara mafiya muni da aka taba gani cikin ‘yan shekarun nan a birnin, wadda a cikin kankanin lokaci ta mamaye wani bene mai hawa 24 a bangaren yammacin London. Sa’o’i da dama a bayan tashin gobarar, ‘yan kwana kwana sun ci gaba da kokarin ceto mutanen da wutar ta rutsa da su cikin ginin, tare da lissafa wadanda suka mutu.

Kwamandan ‘yan sandan birnin London, Stuart Cundy, ya tabbatar da mutuwar mutane 6, amma ya kara da cewa “a bisa dukkan alamu wannan adadi zai karu a yayin da zamu dauki kwanaki da dama muna kokarin nemo gawarwakin wadanda wutar ta rutsa da su.”

Makwabta sun ce sun ji mutane suna ta ihun neman taimako a yayin da wannan wuta ta fara bazuwa daga wannan hawa zuwa waccan, ta rutsa da mazauna ginin wadanda aka gansu ta tagogi suna haska wutar wayoyinsu bisa fatan za a gansu a ceto su.

Benen mai suna Grenfell Tower, yana wata unguwa mai suna North Kensington a bangaren yammacin London. Jami’ai sun ce akwai gidajen haya kimanin 140 a wannan bene, kuma akwai mutane kimanin 500 dake zaune cikinsa. Daga cikin wadanda har yanzu ba a san inda suke ba akwai yara kanana da dama.

A yayin da ginin ya ci gaba da konewa har ya zuwa safiyar yau laraba, an fara neman dalilin da ya sa wannan wuta ta bazu cikin ginin da sauri haka a wannan birni dake da dokoki masu yawa da karfi na hana barkewar gobara irin wannan.

Wasu da suka kubuta daga ginin sun ce basu ji kararrawar dake kadawa idan gobara ta tashi a gini ba.

Masu bincike sun ce ya zuwa yanzu basu san musabbabin gobarar ba, ko kuma dalilin bazuwarta da sauri.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG