Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Muhawara Akan Kayyade Shekarun Tsayawa Takarar Shugaban Kasa A Uganda


Part of the 3 battalion of the Uganda People's Defence Force prepare to leave for African Union peace keeping in Magadishu, Somalia, Friday Sept. 4. 2009, in Entebbe, Uganda. Uganda has sent another group of soldiers to Somalia for a peace keeping mission

Anaci gaba da kai ruwa rana tsakanin jamiyya mai mulki na kasar Uganda da kuma 'yan adawa akan kayyade shekarun tsayawa takarar shugabnan kasa.Domin ko jamiyyar na neman ta cire adadin shekarun tsaya takara dake cikin dokar kasar.

Anci gaba gaba da tafka muhawara mai zafin gaske akan yunkurin jamiyya mai mulki a kasar Uganda na kokarin data keyi na ko a cire adadin shekarun dan takarar shugaban kasa daga cikin dokar kasa.

A cikin wannan satin ne dai ake sa majilisar ta sake tado da wannan maganar tare da ‘yan adawa dake nuna kin amincewar su da wannan batu.

Wakiliyar wannan gidan Radiyon dake aiko da rahotanni daga kasar ta Uganda Halima Althumani tace jamiyya mai mulkin kasar tace zata ci gaba taga cewa ta cire wannan adadin shekaru ga dan takarar shugaban kasa duk ko da yake mutanen kasar sun fito sun gudanar da zanga-zangar nuna kin amincewar su da wannan yunkuri, dama nuna kin yardan ‘yan majilisar dokokin kasar tayi a cikin satin data gabata.

Peter Ogwang shine mataimaki shugaban shugaban jamiyya mai mulki kasar.

Dokar kasarta Uganda dai tasa shekaru 75 ne a matsayin iyakacin shekarun dan takarar shugaban kasa, wannan yana nufin Kenan yanzu haka shekarar 2012 shugaba Yoweri Museveni ba zai iya takara ba.

Masu sukan lamirin wannan batun shekarun sunce wannan tamkar son kai idan jamiyyar tayi haka.

Masu goyon bayan wannan tsarin sunce wanan zai zame wata hanyar da za abi domin mika mulki cikin ruwan sanyi, abinda kasar bata taba samu tun lokacin data samu yanci a shekarar 1962.

‘Yan adawa dai basu da niyyar janye wa daga wannan batu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG