Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Takaddama Tsakanin Ghana Da Nigeria


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Wani rikici da ya kunno kai a tsakanin Najeriya da kasar Ghana ya ja hankalin kwararru a fannin diflomasiya da masu ruwa da tsaki inda su ka yi suka da kakkausar murya tare da neman a dauki kwakkwaran mataki akan kasar Ghana.

Wanan takaddama ta faru ne a lokacin da aka yi amfani da motar rusau wajen tuge wani bangare na ginin ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar Ghana bayan an far ma 'yan Najeriya da ke cikin ginin aka fatattake su har da kwashe kayaiyakin su, bayan da wani mutun ya zo da takardu cewa filin da aka yi ginin nashi ne.

Ma'aikatar hulda da Kasashen Wajen Najeriya ta bakin mai magana da yawun ta Ferdinand Nwonye, ta yi tir da wanan mataki da aka dauka a Ghana inda ya ce ma'aikatar ta gayyaci jakadan kasar Ghana a Najeriya domin ya yi bayanin abinda ya faru har aka kai ga koran 'yan Najeriya tare da rusa Ofishin Diflomasiyarta da ke Ghana.

Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo
Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo

Kwararre a fanin diflomasiyar kasa-da-kasa Ambasada Suleiman Dahiru ya na ganin ba'a taba irin wannan ba a tarihin dangatakar Najeriya da Ghana "saboda haka abu ne da ya sabawa yarjejeniyar diflomasiya ta Geneva da ya ba ire-iren wadannan ofisoshin kariya."

Shi ma shugaban kwamitin majalisar dokoki mai kula da harkokin kasashen waje Yusuf Buba Yakubu ya ce Majalisa ta yi tir da wanan abu kuma za ta dauki matakin duba dokar da ta shafi zamantakewar Najeriya da Kasar Ghana domin wannan shi ne karo na biyu da Ghana za ta yi wa Najeriya wanan cin zarafin. A watannin baya ma Ghana ta kar6e tsohon filin Ofishin jakadancin Najeriya ta baiwa wani banki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG