Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba da Zanga Zanga a Ferguson da Wasu Biranen Amurka


Zanga zanga a Washington, DC kan kasa gurfanarda da Dansandan da ya kashe wanibakatar fata.

A wasu wurare zanga zagar tana tsanani harda kone kone.

A can garin Ferguson dake nan Amurka kuma, an cigaba da ganin zanga-zanga sannan a birane da yawa duk fadin kasa ana ta gangamin goyon baya da bayyana adawa da shawarar da mahukunta suka yanke na rashin samun dalilan gurfanar da wani dan sanda bature a gaban alkali, bayan ya kashe wani bakar fata ba’amurke matashi wanda baya dauke da makami.

Sojojin tsaron kasa sama da dubu 2 ne aka tura garin na Farguson dake jihar Missouri domin tabbatar da zaman lafiya a zanga-zangar dake da nasaba da ban-bancin launin fata, wadda aka fara ran Litinin biyo bayan sanarwar da tace baza a tuhumi dan sanda Darren Wilson ba.

Wakiliyar Muryar Amurka Ayesha Tanzeen wadda a halin yanzu take can garin na Ferguson tace ba’a kuma ga maimaitawar sace-sace ba, kamar yadda aka ga jama’a suna dibar kayan shaguna a daren da aka fara zanga-zangar, har ma aka cinna ma gine gine sama da goma sha wani abu wuta.

XS
SM
MD
LG