Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Zanga-zanga a Kasar Iran


Masu zanga-zanga a Iran
Masu zanga-zanga a Iran

Zanga zangar kin jinin gwamnati ta sake kunno kai da yammacin jiya Lahadi a kasar Iran, dake shiga wuni na biyu na kalubalantar rundunar sojin kasar, wadda da farko ta musunta, daga baya kuma ta amsa harbo jirgin fasinjan Ukraine bisa kuskure, da ya kashe mutane 176 dake cikin jirgin.

Suna karya cewa Amurka ce abokiyar gabar mu, amma makiyan mu na nan cikin kasar, inji wata kungiyar masu zanga-zanga a wajen wata jami’a a Tehran.

Hotunan bidiyo sun nuna masu zanga-zangar a wasu wurare cikin babban birnin da wasu biranen Iran.

‘Yan sandan kwantar da tarzoma sanye da bakaken kaya da hulunan kwano sun fantsama shahararren dandalin Azad dake kudancin tsakiyar birnin da wasu muhimman wurare. ‘Yan sandan sun fita da mesar ruwa da kulake da wasu makamai domin nunawa hukumomi masu zanga zangar. Amma babu wani rahoto nan da nan a kan ko ‘yan sandan sun afka musu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG