Accessibility links

A makon jiya shugaban kasar Najeriya ya tsige ministoci tara yawancinsu daga jihohin da gwamnoninsu suka kafa sabuwar PDP lamarin da ya cigaba da kawo cecekuce.

A makon da ya gabata ne shugaba Jonathan na Najeriya ya ba kasar mamaki yayin da ya tsige ministoci tara lokacin da suke taronsu na mako-mako na majalisar zartaswa.

Tsige ministocin ba zato ba tsammani ya jawo cecekuce a kasar wanda ake gani ba za'a daina yi ba wata kila sai jam'iyyar PDP ta samu masalahar rikicin da ya addabeta. Yayin da wasu ke cewa tsige ministocin ya yi daidai wasu kuma cewa suke babu wani abu cikinsa illa tsagwaran siyasa. Masu cewa tsigensun ya yi daidai domin wai babu abun da suka yi tun lokacin da aka nadasu. Sun kara da cewa gwamnonin dake korafi game da tsige ministocin su ma haka suke yi da kwamisahanoninsu su cire wandada basa so su nada wadanda suke so tamkar suna cin karensu ba babbaka. Da shugaban kasa da gwamnonin doka ce ta basu damar yin hakan da ministoci ko kwamishanoni. A cewar mutanen da suka ce tsigewar ta yi daidai wasu ministocin rikici suka bar wa gwamnatin tarayya.

A mayarda martani bisa ga cecekucen ministan yada labarai Labaran Maku ya ce babu batun siyasa ciki kuma babu batun ko sun iya aiki ko basu iya ba. Sun yi aiki shekara biyu sai a godewa Watakila shugaban kasa ya dauki matakin ne domin ya sake alkiblar gwamnatinsa.

Masu cewa tsigesu nada nasaba da siyasa sun ce me yasa sai yanzu za'a tsigesu. Suka ce wasu daga gwamnoni bakwai ne da ke takunsaka da jam'iyyarsu suka bada sunayensu lokacin da aka nada su dalili ke nan aka ciresu. Wasu kuma sun ce akwai ministocin dake neman tsayawa takara a jihohinsu yayin da ake ganin akwai wasu kuma da basu da tasiri a kokarin shugaban kasa na son sake tsyawa takar zabe a shekarar 2015. Daya daga cikin ministocin wanda gwamnatin ta gada daga gwamnatin Yaradua an ce baya ma shiri da gwamnan jiharsa amma kuma ba zai yi wani tasiri ba a zaben shugaban kasa. Wasu sun ce idan tsigewar na da nasaba da siyasa to ministan dake da dangantaka mai kyau da matar shugaban kasa fa kuma ta dalilinta ya zama minista.

A wani abu kuma mai ban mamaki an ce an ga wasu ministocin suna kwalla lokacin da suke mika takardar barin aiki. Amma Muryar Amurka ta jiwo ministar ilimi da aka tsige tana jawabi a wani gagarumin taro da aka shirya mata a jiharta tana cewa ya kamata a godewa shugaban kasa da zarafin da ya bata lokacin da gwamnanta ya gabatar da ita gareshi. Ta ce ya karbeta hannu biyu biyu. Ta ce a ma'aikatar ilimi yawancin ministocin basa dadewa. Wasu na shekara daya wasu kuma basa wuce shakara biyu. To amma ita ta yi shekara uku da rabi.

Gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya ce abun dake faruwa bashi da nasaba da abun dake faruwa a jam'iyyarsu. Rudanin jam'iyyarsu ta PDP ya sha ban-ban da tafiyar da harkokin gwamnati. Ya ce ba zamu iya gina kasa mai daraja ba idan kome aka yi za'a kalleshi da fuskar siyasa. Abun da shugaba ya yi yana cikin ikonsa da kundun tsarin mulki ya bashi.

Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.

XS
SM
MD
LG