Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana cigaba da neman gawarwaki a inda wani jirgin sama ya yi hadari a Nijeriya


Jirgin saman da ya fadi a Nijeriya

Masu ayyukan ceto a Nijeriya sun zakulo gawarwaki 137 daga baraguzan

Masu ayyukan ceto a Nijeriya sun zakulo gawarwaki 137 daga baraguzan jirgin zaman da ya rikito kan wasu gidajen jama’a a Lagos ranar Lahadi.

Dukkannin mutane 153 da su ka hada da fasinjoji da matuka jirgin sun halaka hade da wasu mutanen da ke kasa da ba a san adadinsu ba.

Daga cikin gawarwakin da aka gano har da na wata uwa da ke rungume da danta. Masu ayyukan ceto sun ce da yawa daga cikin wadanda abin ya rutsa da su sun kone kurmus.

Kaftin din jirgin saman ya aike da rahoto kan matsalar injin dab da faduwar jirgin. To amman mai bai wa Shugaban Kasar Nijeriya Shawara game da ‘yan jarida Reuben Abati ya gaya wa Sashen Turanci na Muryar Amurka cewa za a yi riga malam masallaci idan aka ce ga abinda ya haddasa hatsarin a halin yanzu.

Ya ce, “Abin da Shugaban Kasa ya yi, dadin dadawa, shi ne ya bayar da umurnin gudanar da bincike ba tare da bata lokaci ba kan musabbabin hadarin. Ina ganin abin da ya kamata shi ne ka jira sakamakon binciken. A halin da ake ciki a yanzu kowa na cikin kaduwa, ciki har da Shugaban Kasa, kuma abin da ka ke gani shi ne wata al’ummar da ke cikin bakin ciki.”

Shugaba Goodluck Jonathan ya ware ranaku uku don makoki a hukumance. Ya ziyarci wurin da abin ya faru sannan ya yi alkawarin cewa wannan irin bala’in ba zai kara faruwa ba, tare da alkawarin inganta tsaron lafiya a sufurin jirgin sama.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Mark Toner ya ce Amurka na mai aikewa da sakonta na matukar juyayi ga wadanda su ka rasa kaunatattunsu a hadarin.

Jirgin na kamfanin jirgin saman Dana na tafiya Lagos ne daga Abuja yayin da ya fada kan wani bene mai hawa biyu a wurin da ke cunkushe da jama’a, ya janyo gobara a wasu gine-ginen.

Kamfanin na “Dana Airlines” wani kamfanin zirga-zirgar jirgin sama da ke harka cikin kasar ne da rukunin jiragen sama samfurin Boeing MD-83 daga Abuja zuwa Lagos, tsawon awa guda.

XS
SM
MD
LG