Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba da Zanga Zanga a Misra


Masu zanga-zangar kin gwamnati a Misra.

Masu zanga a Misra sun cigaba da kiraye-kirayen Shugaba Hosni Mubarak ya sauka daga gadon mulki

Masu zanga a Misra sun cigaba da kiraye-kirayen Shugaba Hosni Mubarak ya sauka daga gadon mulki, a daidai lokacin da hukumar sojin kasar ke kiran masu zanga-zangar su koma harkokinsu na yau da kullum.

Daruruwan masu zanga-zanga sun cigaba da zama a Dandalin Tahir zuwa yau Talata, inda mutane wajen 250,000 su ka taru jiya su na kiran Mr. Mubarak ya yi murabus.

Shugaban na Misra ya sanar jiya Talata cewa ba zai sake tsayawa takara ba a zaben watan Satumba to amman ya sha alwashin kammala wa’adinsa.

Hukumar sojin kasar ta fitar da wata sanarwar da aka yada ta gidajen talabijin a yau Laraba cewa an saurari sakon masu zanga-zangar kuma an fahimci bukatunsu.

Wasu daruruwan mutanen kuma sun yi gangamin goyon bayan Mr. Mubarak a babban birnin kasar.

Dadadden shugaban na Misra ya fadi a gidan talabijin din gwamnatin kasar cewa duk tsawon rayuwarsa ya bauta wa Misra ne da mutanen Misra, ya kuma yi alkawarin yin amfani da sauran lokacinsa wajen tabbatar da mika ragamar iko cikin kwanciyar hankali.

Nan da nan bayan jawabin na Mubarak, sai aka shiga arangama tsakanin masu zanga-zangar da magoya bayan gwamnati a birnin Aksandariya da ke kusa da gabar teku a arewacin kasar. Akalla mutane 12 sun sami raunuka. Shaidun gani da ido sun bayar da rahotannin irin wannan al’amarin a Suez da wasu biranen gabashin al-Khahira.

A halin da ake ciki kuma, kafar sadarwar intenet ta soma aiki a kasar a yau Laraba bayan matsalolin kwana da kwanaki kuma irin wadanda ba a taba gani ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG