Masu neman sayen tikitin jirgin kasa zuwa Abuja daga Kaduna sai sun yi hargowa akan layi kuma sau tari wasu ma ba zasu samu tikitin ba.
Ture ture da nufin samun tikitin zuwa babban birnin tarayya Abuja a jirgin kasa na tasowa ne, saboda irin wahalar da wasu keyi wajen sayen tikitin inda sukan kwashe sa'o'i biyu zuwa uku amma daga bisani su tashi a tutar babu. Amma wasu sukan zo dap da lokacin da jirgin zai tashi kuma su samu tikitin tafiya.
Rahotanni sun ce a makon jiya farashin tikitin zuwa Abuja sai da ya ninka uku. Maimakon Nera 1300, sai da aka sayeshi sama da Nera 4000 domin a tafi Abuja.
Binciken da Sashen Hausa na Muriyar Amurka ya giudanar ya nuna farashin bai ninka ba a makon nan da ya gabata, saboda wasu da aka turo daga hukumar jirgin kasa daga Lagos domin su binciki zargin cuwa cuwar da ake yi.
Wasu matafiya sun fito tun karfe goma maimakon karfe dayan da jirgin zai tashi amma har zuwa lokacin da jirgin ya tashi wasunsu ba su samu tikitin ba saboda ba'a fara sayer da tikitin ba sai da misalin karfe 12, kuma bayan minti 30 aka fada masu tikitin ya kare. Amma an ci gaba da sayar da tikitin ta bayan fage har zuwa minti biyar kafin jirgin ya tashi.
Wani da bai samu tikitin ba ya yi karin haske akan hada-hadar tikitin da ake fama da ita. Ya ce rashin samun tikiti ba sabon abu ba ne. Sau tari tikitin da ake sayarwa N1300 sai a ga ana sayar dashi a bayan fage N2000 ko 2500.
Dangane da magance wannan matsalar, wani fasinja ya ce a maida sayar da tikitin ta yanar gizo ta yadda ko daga gida mutum na iya saya. A tashar kuma sai mutum ya yi anfani da yanar gizo ya saya.
Yunkurin da Sashen Hausa ya yi na jin ta bakin manya jami'an tsahar ya cutura saboda wai an turo masu masu binciken daga Ikko kan batun sayar da tikitin. Daya daga cikin wadanda aka turo daga Lagos ya ce ba zai yi magana ba sai ya samu izini.
A saurari rahoton Isa Lawal Ikara domin karin bayani
Facebook Forum