Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Dab Da Kada Kuri'ar Tabbatar da Brett Kavanough


Shugaban kwamitin shari'a Chuck Grassley tare da Brett Kavanaugh,

Ana dab da shiga matakin karshe na tabbatawr da alkali Brett Kavanough ya cike gurbin kujerar alkalin kotun kolin Amurka, yayinda ake kyautata zaton kada kuri’ar karshe ranar asabar.

Da farko dai, sanatocin zasu yi nazarin rahoton da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI bisa zargin da ake yiwa Kanavough na cin zarafin wata mace lokacin suna matasa, da kuma zargin cewa ya nuna tsiraicinsa gaban wata mata lokacin suna jami’a.

Kavanaugh ya musanta zargin.

Shugaban kwamitin harkokin shari’a na majalisar dattijai Chuck Grassley ya bayyana yau alhamis cewa, kwamitin ya karbi rahoton binciken hukumar FBI, kuma shi da daya daga cikin kusoshin jam’iyar Democrat Dianne Feinstein sun amince za a ba dukan bangarorin dama su yi nazarin bayanan .

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG